Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Minstan lafiyar ya ce asibitotcin Labanon cike suke da wadanda hare-haren suka rutsa da su, wanda hakan ke nuna wadanda suka yi shahada da jikkata suna da yawa. Isra’ila ta kai hare-hare sama 100 a sassa daban-daban na kasar Lebanon tun da safiyar yau, ciki har da Beirut da Sidon. Yawan shahidai da wadanda suka jikkata ya yi yawa sosai.
An kashe daruruwan mutane tare da raunata wasu sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai a fadin kasar Lebanon. Sannan Isra’ila ta kai wa gidan Nabih Berri, kakakin majalisar dokokin Lebanon hari duk da cewa: Majiyoyin Lebanon sun ba da rahoton tabbacin lafiyar kakakin majalisar dokokin kasar Labanon, Nabih Berri, duk da hare-haren da Isra'ila ta kai a sassa daban-daban na Lebanon, ciki har da Ain Al-Tina, mahallin kakakin majalisar. Mummunan hare-haren bama-baman ta sama da Isr’aila ta kai d a yankunan kudancin birnin Beirut a fiye da wurare 100 a Lebanon cikin mintuna 10. Wanda wadannan wuraren sun hada harda da kaburburan Hizbullah ta Lebanon a Beirut bayan hare-haren Isra'ila da dama. Sanna Isra’ila ta rushe wuraren zama da dama a Lebanon.
Harin bama-bamai mafi muni a Lebanon tun bayan da kungiyar Hizbullah ta shiga yakin kare Iran. Shahadar fiye da 300 na Lebanon a cikin mummunan harin bam na gwamnatin Sahayoniya ta kai kasar. Firayim Ministan Lebanon: Isra'ila ba ta damu da duk wani ƙoƙarin zaman lafiya na yanki ko na duniya don dakatar da yakin ba.
Your Comment